<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>219</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Cikin sunan Ubangiji,
 Kullum zan yi ta aikina.
 Muradina saninka ne,
 Cikin duk al'amurana.

[V2]
 2) Tsare ni daga tarkoki,
 Ɓoye rarraunar zuciyata,
 Kada ta faɗa nishaɗi
 Wanda ke cikin duniya.

[V3]
 3) Kai ne a hannun damana,
 Kai idona ke dubawa,
 Domin in bi umarninka
 Wanda ka nufe ni da yi.

[V4]
 4) Ɗawainiyarka mai sauƙi ce,
 Kayanka ba mai nauyi ba,
 Taimake ni in jure fa,
 Har ran da zan kai mulkinka.

[V5]
 5) Wanda ya zo, ka karƃe shi,
 Domin ya dinga aikinka.
 Don haka murna na ke yi,
 Har ran da zan je can Sama.</lyrics>
<title>Cikin Sunan Ubangiji LW219</title>
</song>